Dr. Lawal Ahmad: Cire Tallafi da Ƙara Haraji a Lokaci Guda Kuskure ne – Wani Nau’i ne na Danƙarar da Talaka
A wani rubutu da Dr. Lawal Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi kakkausar suka ga matakan gwamnati na cire tallafin man fetur (subsidy) tare da ƙara haraji a lokaci guda, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin tsari, rashin lissafi, da kuma rashin tausayi ga talaka.
“La’akari da cire subsidy da kuma saka haraji lokaci guda na nuna cewa mahukuntan ba su yi cikakken tunani ba,” in ji Dr. Lawal.
Haraji ba Sabon Abu ba, Matsalar Ita ce Rashin Amfani da Shi yadda Ya Kamata
Dr. Lawal ya jaddada cewa biyan haraji ba shi ne matsala ba, domin tun da daɗewa ‘yan ƙasa suna biyan haraji iri-iri — a kasuwa, a kan hanyoyi, a rajista, da ma a kan motoci.
Sai dai matsalar ita ce:
“Ana biyan haraji, amma yawanci yana karewa ne a aljihun wasu, ba a gani a aikin raya kasa, ilimi ko kiwon lafiya.”
A cewarsa, ƙasashen da ke amfani da haraji wajen bunƙasa tattalin arzikinsu su ne waɗanda ke da tsari, gaskiya, da cikakken sa ido kan yadda ake kashe kuɗin jama’a abubuwan da ya ce har yanzu ba su inganta yadda ya kamata ba a Nijeriya.
Ina Riba Idan Babu Accountability da Doka?
Wani muhimmin sako da D.r Lawal ya jaddada shi ne rashin gaskiya da rashin bin doka (rule of law) a cikin tsarin tafiyar da dukiyar jama’a.
Ya ce:
“Meye amfanin haraji a kasar da babu accountability, babu hukuma mai tsayuwa ta bincike da hukunta masu almubazzaranci da duniyoyin al'umma?”
A ganinsa, cire tallafi da ƙarin haraji ba wai gyara ba ne, illa wata dabara ce da za ta ƙara jefa talaka cikin ƙunci, tare da rugujewar ƙananan sana’o’i da masu dogaron kasuwanci.
“Ba Wata Kasa da Haraji Ya Gina Tattalin Arzikinta Shi Kadai”
Dr. Lawal ya ƙi amincewa da ra’ayin da ke cewa haraji zai gyara tattalin arzikin Nijeriya. Ya ce babu wata kasa a duniya da ta taɓa dogaro da haraji kaɗai wajen bunƙasa tattalin arziki.
A cewarsa, abin da ke gina kasa shi ne:
- Samar da masana’antu
- Inganta noma
- Tabbatar da tsaro
- Ƙirƙirar ayyukan yi
- Gaskiya a mulki
Ya kuma bayyana tsoronsa na cewa, shawarwarin da ake bi yanzu na iya kasancewa daga kasashen yamma, ba tare da la’akari da halin da ‘yan kasa ke ciki ba.
Da dama mutane sun nuna damuwarsu game da tsadar rayuwa, tashin farashin kayayyaki, da fargabar yadda kasuwanci ke fuskantar barazana.
Wasu na kira da a duba hanyoyin sauƙaƙa wa jama’a, yayin da wasu ke nema a samu cikakken bayani daga gwamnati kan yadda za a kashe kuɗaɗen da aka tara daga haraji.
Tambayar da Har Yanzu Bata da Amsa
Ra’ayin Dr. Lawal ya bar muhimmiyar tambaya a zukatan mutane:
Shin cire tallafi da ƙara haraji zai gina ƙasa ne, ko kuwa zai karya bayan talaka?