Shinkafa Ta Bar Baya Da Kura: Takaddama Ta Barke A Kannywood
Wata sabuwar baraka ta kunno kai a masana'antar fina-finan Hausa (Kannywood), wacce ta kusa kaiwa ga sanya "Baiwa Hammata Iska." Lamarin ya faro ne bayan jarumi Nuhu Abdullahi yayi rabon tallafin shinkafa ga wasu daga cikin abokan aikinsa, lamarin da ya raba kawunan jaruman gida biyu: Masu "Tuwo na Maina" da kuma masu "Kishin Darajar Jarumai."
Taron rabon shinkafar, wanda ya hada fuskokin manya da kananan jarumai, ya haifar da ce-ce-ku-ce. Wasu tsaffin hannu a masana'antar sun nuna bacin ransu, suna ikirarin cewa raba wa jarumi shinkafa a gaban kyamara kamar ana raba wa mabarata ne, hakan yana rage musu kima a idon duniya. Suka ce, "Jarumi ya wuce matsayin mai jiran kwanon awo."
Nuhu Abdullahi bai yi kasa a gwiwa ba, inda ya mayar da martani da kakkausan harshe ga wadanda suka fara sukar lamarin, musamman mawaki Ali Jita da abokinsa Bifa. Fadan ya koma na salon "wa ya isa," inda aka fara musayar kalamai masu zafi a kafafun sada zumunta.
Ba a tsaya nan ba, domin jarumi Abale (Saraki) ya shigo cikin zancen da nasa salon. Shi da Aminu J. Town tare da Soja Boy, sun ja layi ja. Abale ya bayyana cewa duk wanda ya kuskura ya kara sukar maganar shinkafar, to zai hadu da fushinsa.
Wannan furucin nasa ya sa jama'ar gari suka yi masa lakabi da sabon sarauta: "Sarkin Shinkafar Kasar Hausa."
A gefe guda kuma, mawaki Garzali Miko ya fito fili ya bayyana matsayinsa ba tare da tsoro ba. Yana mai cewa:
"Ni dai muddin ana rabon shinkafa, ko ana ruwan kibiyoyi sai na karba. Matar gida tana jirana, kuma tukunyar gidanmu ba ta san 'darajar jarumi' ba, shinkafa take sani!"
Ita dai wannan shinkafa ta Nuhu Abdullahi, ta riga ta bar baya da kura. Masu sharhi na ganin cewa hakan wata alama ce ta rashin hadin kai ko kuma nuna halin da masana'antar take ciki na rashin tabbas.
Yayin da wasu ke ganin tallafin a matsayin "Alkhairi," wasu na kallonsa a matsayin "Sarcasm" da kuma wulakanci ga wadanda suka dade suna gina martabar Kannywood.