A ka'ida ta likitanci, babu wata doguwar takaddama kan takaimaiman tana ko lokacin da ya kamata a koma jima'i bayan an samu haihuwa, amma mafi yawancin likitoci suna bayar da shawarar jiran makonni 4 zuwa 6 (wato kwanaki 30 zuwa 40) bayan haihuwa kafin a koma ga jima'i.
Wannan lokaci zai baiwa mahaifiya ƙarin Nutsuwa tare da baiwa sauran sassan jikin uwa samun damar komawa asalin yadda suke
Dalilan Da Suke Sanya A Jira Na Tsayin Wannan Lokaci
Akwai manyan dalilai na lafiya da suka sa aka kayyade wannan lokaci:
1. Warkewar Mahaifa: Bayan an haifi jariri da mahaifa (placenta), da akwai babban rauni da ke baruwa a cikin mahaifar mace. Yana daukar makonni kafin wannan rauni ya warke kuma kofar mahaifa (cervix) ta koma yadda take ta rufe.
2. Tsayawar Jinin Haihuwa (Lochia): Mace tana ci gaba da zubar da jini ko wasu ruwaje bayan haihuwa. Matukar wannan jini bai tsaya gaba daya ba, komawa jima'i na iya janyo kwayoyin cuta (infections) cikin sauki.
3. Warkewae da Dinki ko Tsagewa: Idan an yi wa mace dinki saboda tsagewar gaba (episiotomy) ko kuma raunin fiɗa wato (C-S), dinkin yana bukatar lokaci domin ya bushe kuma ya juye. Jima'i da wuri na iya tsitstseke dinkin ko janyo zafi mai tsanani.
Kalubalen Da Za A Iya Fuskanta Lokacin Dawowa
Yana da kyau ma'aurata su sani cewa komawa jima'i bayan haihuwa na iya fuskantar wasu canje-canje:
1. Bushewar Gaba (Vaginal Dryness): Saboda canjin kwayoyin halitta (hormones), musamman ga uwa mai shayarwa, gaban mace yana iya yin bushewa sosai. Wannan na iya sa jima'i ya kasance mai zafi.
2. Gajiyar Jiki da Rashin Bacci: Kulawa da jariri na bukatar kuzari sosai, wanda hakan ke rage sha'awar jima'i ga ma'auratan biyu a farko-farko.
3. Tsoro da Fargaba: Mata da dama suna fuskantar tsoron cewa zafi zai musu, ko kuma dinkinsu zai fashe.